Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Warin Safa Yana hana Yaduwar Zazzabin Cizon Sauro


Hoton sauro

Masu bincike a Afirka sun gano cewa safar kafa mai wari tarko ne ga sauro, wadda zai iya taimakawa wajen rage yaduwar cutar zazzabin cizon sauro ko malaria.

Masu bincike a Afirka sun gano cewa safar kafa mai wari tarko ne ga sauro, wadda zai iya taimakawa wajen rage yaduwar cutar zazzabin cizon sauro ko malaria.

Dr. Fredros Okumu na cibiyar kiwon lafiya da ake kira Ifakara a Tanzania, yace a wani gwaji da suka yi kwana kwanan nan, ya nuna cewa warin safar yana janyo hankalin sauro su fada raga fiyeda dan’dama dake kwance a kurkusa.

Dr. Okumu yace masana kimiyya sun jarraba haka ne a wani kauye inda suka kwai-kwayi warin safa wadda ya janyo sauro suka shiga kwalaye da aka fesa musu magani.

Gidauniyar Bill da Melinda Gates da kuma wata irinta a Canada sun baiwa likitan gudumawar dala dubu 775 domin ya ci gaba da binciken kan wan nan lamari.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG