Accessibility links

An bada belin mutumin daya kashe wani bakar fata a Florida

  • Jummai Ali

George Zimmerman

An bada belin George Zimmerman, mutumin daya kashe wani bakar fata a Florida akan dala dubu dari da hamsin

An bada belin George Zimmernan, mutumin nan da aka caja da laifin kashe Trayvon Martin wani matashi dan shekara goma sha bakwai a Florida nan Amirka.

Da tsakar daren jiya Lahadi, aka bada belin Zimmerman akan kudi dala dubu dari da da hamsin. A ranar juma’a aka bada belinsa, kuma alkalin daya bada belinsa ya umarce shi, daya mutunta ka’idodin dokar hana fita da aka aza masa.

Ba’a san inda aka kai Zimmerman kafin a fara yi masa shari’a ba. Amma tilas ya sanya wata na’urar lura da inda yaje. An caji George Zimmerman da laifin kashe Trayvon Martin a ranar ashirin da shidda ga watan Fabrairu.

Wannan al’amary ya hadasa zanga zangar nuna rashin amincewa a duk fadin Amirka. Da farko yan sanda basu kama Zimmerman bayan ya harbe Trayvon ba, domin yayi ikirarin cewa ya kare kansa ne.

XS
SM
MD
LG