Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan takarar jam'iyar gurguzu Francis Hollande yana kan a gaba zaben Faransa


Dan takarar jam'iyar guguzu Francois Hollande

Dan takarar jam’iyyar gurguzu a zaben shugaban kasa na Faransa, Francois Hollande, yana kan gaba a zagayen farko na zaben da aka yi jiya lahadi.

Dan takarar jam’iyyar gurguzu a zaben shugaban kasa na Faransa, Francois Hollande, ya zamo a kan gaba a bayan da ya doke shugaba Nicolas Sarkozy a zagayen farko na zaben da aka yi jiya lahadi.

Sakamakon farko da hukumomi suka bayar ya nuna Hollande a kan gaba da kashi 29, yayin da shugaba Sarkozy mai ra’ayin ‘yan mazan jiya yake da kashi 26 cikin 100 na kuri’un. Mutanen biyu zasu sake karawa da juna a zaben fitar da gwani ranar 6 ga watan Mayu.

Wasu ‘yan takarar su 8 sun kasance a can baya. Amma ‘yar takara Marie le Pen mai matsanancin ra’ayin rikau tare da akidar hana baki zama a kasar, ta ba ‘yan kallo mamaki a lokacin da ta zo ta uku da kuri;un da suka zarce kashi 10 cikin 100.

Hollande ya bayyana kansa a zaman mutumin da ya fi dacewa ya zamo sabon shugaban Faransa. Yace yana son ya hada kan abinda ya kira kasar da ta samu rarrabuwar kawuna a saboda manufofin da suka kasa aiki na shugaba Sarkozy. Har ila yau yace yana son ya kara yawan harajin da attajirai ke biya.

Mr. Sarkozy yace yace ya fahimci masu jefa kuri’a na Faransa sun damu a wannan lokaci na rikici, ciki har da damuwa kan tattalin arziki da aikata laifuffuka. Ya kalubalanci Hollande da su zo suyi muhawara har sau uku a kan kula da jin dadin rayuwar jama’a, da tattalin arziki da kuma batutuwan kasa da kasa kafin zaben fitar da gwanin na ranar 6 ga watan Mayu.

XS
SM
MD
LG