Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bai Wa Hamata Iska a Wajen Gangamin Fifita Jinsin Turawa a Virginia


An yi arangama tsakanin wasu turawa masu gangamin fifita jinsinsu da wasu masu adawa da wannan gangamin a jihar Virginia.

An bai wa hammata iska yau asabar a wurin wani gangami na turawa jar fata masu fifita jinsin turawa da kuma ‘yan zanga zangar da suka fito yin adawa da wannan gangamin a Jihar Virginia dake makwabtaka da nan Gundumar Colombia.

Hotunan bidiyo na wannan arangamar sun nuna Turawa ‘yan wariyar launin fata dauke da garkuwa da kulakai, suna musanyar bugu da masu adawa da su, su ma dauke da nasu kulakai da garkuwa lokacin wannan maci da aka yi a birnin Charlottesville.

An yi ta bai wa hammata iska kafin ‘yan sanda su kutsa cikin lamarin, inda suka bayyana wannan gangami a zaman taro na haramun, suka kuma fara korar mutane daga wurin.

Gwamna Terry McAuliffe na Jihar Virginia ya fada a shafinsa na Twitter cewa ya ayyana dokar ta baci a biornin domin hukuma ta samu sukunin takalar wannan tashin hankali a wurin gangamin na Turawa ‘yan wariyar launin fata a Charlottesville.

Tun da fari, gwamnan na Virginia ya gargadi mutane da su kaucewa zuwa harabar Jami’ar Virginia, inda ‘yan ra’ayin wariyar launin fatar suka shirya gudanar da wannan gangami wanda aka lakaba wa suna Gangamin hada Kan Masu ra’ayin Rikau.

A jiya da daddare ma sai da aka gwabza a tsakanin wasu turawa ‘yan wariyar launin fata dake dauke da fitilu da wasu masu adawa da wannan akida da su ma suka fito. Sai da ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa gangamin.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG