Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bayyana Gwarzayen Da Suka Sami Lambar Yabon 'Yan Wasan FIFA na 2021

Lionel Messi na cikin jerin sunayen da kwamitin da FIFA ta nada.
Lionel Messi na cikin jerin sunayen da kwamitin da FIFA ta nada.

Messi, Ronaldo, Mbappe, da Lewandowski suna cikin jerin sunayen ‘yan wasan da FIFA ta fitar da za ta ba kyautar gwarzon dan wasa na shekara.

Chelsea ta lashe gasar zakarun Turai sannan Ingila ta kai wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai, amma babu wani dan kasar Ingila da ke cikin jerin sunayen ‘yan takarar da FIFA ta fitar a ranar Litinin.

Robert Lewandowski na Bayern ya yi murnar zura kwallo ta biyu a wasan kwallon kafa na Bundesliga na Jamus tsakanin FC Bayern Munich da SC Freiburg a Munich, Jamus, Asabar, 6 ga Nuwamba, 2021.
Robert Lewandowski na Bayern ya yi murnar zura kwallo ta biyu a wasan kwallon kafa na Bundesliga na Jamus tsakanin FC Bayern Munich da SC Freiburg a Munich, Jamus, Asabar, 6 ga Nuwamba, 2021.

Jorginho, wanda ya kasance zakaran Turai sau biyu a Chelsea da Italiya, a tare da abokin wasansa N’Golo Kanté suna cikin 'yan takara 11 da za a zaba a matsayin gwarzon dan wasa na FIFA a wasar ta 2020-21.

Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun shiga jerin sunayen kamar yadda suka saba shiga da Robert Lewandowski wanda ya zama zakara bara.

Mohamed Salah, Kylian Mbappé, Erling Haaland, Kevin De Bruyne, Karim Benzema da Neymar suna cikin jerin sunayen da kwamitin da FIFA ta yanke.

Jorginho na Italiya ya ba da kwallon yayin da Remo Freuler na Switzerland ya rufe shi a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na rukunin C na 2022 tsakanin Italiya da Switzerland a filin wasa na Olympics na Rome, Juma'a, 12 ga Nuwamba, 2021.

Babu masu tsaron gida da ke jerin wadanda za a zabi zakara domin wannan babbar kyautar FIFA, ko da yake masu tsaron gida suna da tasu kyautar.

Gianluigi Donnarumma na Italiya, wanda aka zaba a matsayin gwarzon dan wasa a gasar Euro 2020, yana daga cikin ‘yan takarar masu tsaron gida biyar.

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohamed Salah na murnar zura kwallo ta uku a wasan da kungiyarsa ta buga tsakanin Liverpool da Arsenal a filin wasa na Anfield, dake kasar Ingila, Asabar, 20 ga watan Nuwamba, 2021.

Za a tattara kuri'u daga kyaftin din tawagar kasar da masu horarwa, magoya baya da kafafen yada labarai na duniya har zuwa ranar 10 ga Disamba.

Za a gudanar da wani biki a ranar 17 ga Janairu ta hanyar intanet, daga hedkwatar FIFA da ke Zurich saboda cutar ta COVID-19.

Gwarzayen 'yan wasan maza na FIFA:
Karim Benzema (France / Real Madrid CF)
Kevin De Bruyne (Belgium / Manchester City FC)
Cristiano Ronaldo (Portugal / Juventus FC / Manchester United FC)
Erling Haaland (Norway / BV Borussia 09 Dortmund)
Jorginho (Italy / Chelsea FC)
N’Golo Kanté (France / Chelsea FC)
Robert Lewandowski (Poland / FC Bayern München)
Kylian Mbappé (France / Paris Saint-Germain)
Lionel Messi (Argentina / FC Barcelona / Paris Saint-Germain)
Neymar (Brazil / Paris Saint-Germain)
Mohamed Salah (Egypt / Liverpool FC)

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG