Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Messi Bai Zura Kwallo Ba Har Yanzu – Masu Sharhi


Lionel Messi

Sai dai akwai wadanda suka yi hasashen cewa, Messi zai farfado kuma zai taka rawar gani a sabuwar kungiyar tasa ta PSG yayin da suke shirin karawa da Manchester City.

Masoya kwallon kafa na ci gaba da laluben dalilin da ya sa Lionel Messi bai zura kwallo ko daya ga sabuwar kungiyarsa ta PSG ba.

A watan Agusta Messi ya koma kungiyar ta Ligue 1 da ke Faransa, bayan da aka samu akasi wajen sabunta kwantiraginsa a Barcelona, lamarin da ya sa Messi ya fice a kungiyar cikin wani yanayi mai cike da alhini.

Sai dai ba kamar Cristiano Ronaldo da shi ma ya fice daga Juventus ta Italiya ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United ba, Messi har yanzu bai zura kwallo ko daya ba.

Tuni Ronaldo ya ci kwallaye hudu ga Manchester United a wasanni daban-daban da ya buga mata.

Messi ya bugawa PSG wasannin uku, daya daga ciki ne kadai ya buga minti 90 cif, yayin da wasansa na farko da Reims ya shiga a matsayin dan canji inda ya buga minti 25.

A halin da ake ciki Messi dan shekara 34 na fama da ‘yar jinya a gwiwa kuma akwai alamu da ke nuna cewa har yanzu bai dawo cikin cikakken hayyacinsa ba tun bayan barin Barcelona.

Messi a lokacin wasansu da Reims
Messi a lokacin wasansu da Reims

“Shi Lionel Messi, tun yana yaro, yana Barcelona ne, saboda haka, yadda ake buga wasa a Faransa da Sifaniya (Spain) ba daya ba ne, shi ya sa abin ya zama masa sabo.” In ji mai sharki akan kwallon kafa Ishola Michael.

A cewar Michael, Messi ya yi wasanni uku amma har yanzu bai zura kwallo ko daya ba, “amma ka kalli Ronaldo yana da kwallaye, Lukaku ma yana da kwallaye.”

“Da ma an jima ana muharawa kan ko Lionel Messi zai iya kwallo kuwa idan ya bar Barcelona, to ka ga zahiri yanzu maganar ta fara fitowa karara.” Michael ya ce.

Sai dai akwai wadanda suka yi hasashen cewa, Messi zai farfado kuma zai taka rawar gani a sabuwar kungiyar tasa ta PSG.

“Bai daidai ba ne a ce bai tabuka komai ba, saboda tabbas ya yi abin a-zo-a-gani, amma nan ba da jimawa ba asalin wasansa zai fito fili.” In ji Lawrence, wani masoyin Messi.

Tuni dai kungiyar ta tabbatar da cewa Messi na daya daga cikin ‘yan wasan da za su tunkari ‘yan wasan Pep Guardiola a wasan cin kofin zakarun nahiyar turai ta UEFA.

Paris Saint Germain za ta karbi bakunci Manchester City wacce kocinta Guardiola ya horar da Messi a Barcelona.

A wasanta na karshe, PSG ta doke Montpellier da ci 2-0 a gasar Ligue 1.

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG