Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bayyana Ma'aikatun Da Sabbin Ministoci Zasu Jagoranta An Ba Solomon Dalong Ma'aikatar Matasa Da Wasanni


Ministan Sufuri Rotimi Ameachi da suna gaisawa da Shugaba Buhari.

A wani matakin ba-zata, an ba tsohon babban hafsan sojojin kasa, Abdul-Rahman Dambazau, ma'aikatar harkokin cikin gida, yayin da tsohon gwamnan Jihar Rivers Rotimi Amaechi ya zamo sabon ministan harkokin sufuri.

A bayan da ya rantsar da sabbin ministocinsa a yau laraba a fadar Aso Villa, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana ma'aikatun da wadannan ministocin zasu shugabanta.

Dan rajin kare hakki da yaki da zarmiya da cin hanci, Solomon Dalong, ya zamo ministan wasanni da harkokin matasa, yayin da a wani matakin ba-zata aka nada tsohon janar Abdul-Rahman Dambazau, tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, a zaman ministan harkokin cikin gida.

Wani tsohon hafsan sojan, Birgediya-Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, shi ne ya zamo sabon ministan tsaro.

Sauran manyan ministocin da aka ba ma'aikatu a yau din sun hada da tsohon gwamnan Jihar Rivers Rotimi Amaechi, wanda aka ba ministan sufuri; tsohon gwamna Babatunde Fashola na Jihar Lagos wanda aka ba ministan Wutar Lantarki, Ayyuka da gidaje; Abubakar Malami, ministan shari'a.

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Rantsar Da Ministoci - 3'26"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

Ga cikakken jerin sunayen ministocin, da jihohin da suka fito, da ma'aikatunsu:

 • Abubakar Malami (Kebbi) - Shari'a
 • Geoffrey Onyeama (Enugu) - Harkokin Waje
 • Khadija Bukar Abba (Yobe) - Karamar Minista, Harkokin Waje
 • Babatunde Fashola (Lagos) - Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje
 • Mustapha Shehuri (Borno) - Karamin Minista, Wutar Lantrarki, Ayyuka da Gidaje
 • Rotimi Amaechi (Rivers) - Sufuri
 • Chris Ngige (Anambra) - Kwadago da Samar Da Ayyukan Yi
 • James Ocholi (Kogi) - Karamin Minista, Kwadago da Samar Da Ayyukan Yi
 • Kayode Fayemi (Ekiti) - Ma'adinai
 • Abubakar Bwari Bawa (Niger) - Karamin Minista, Ma'adinai
 • Abdulrahman Dambazau (Kano) - Harkokin Cikin Gida
 • Aisha Alhassan (Taraba) - Harkokin Mata
 • Ogbonnaya Onu (Ebonyi) - Kimiyya da Fasaha
 • Kemi Adeosun (Ogun) - Harkokin Kudi
 • Hadi Sirika (Katsina) - Karamin Minista, Zirga-Zirgar Jiragen Sama
 • Suleiman Adamu (Jigawa) - Albarkatun Ruwa
 • Solomon Dalong (Plateau) - Matasa da Harkokin Wasanni
 • Muhammadu Buhari - Albarkatun Man Fetur
 • Ibe Kachikwu (Delta) - Karamin Minista, Albarkatun Man Fetur
 • Isaac Adewole Folorunsho (Osun) - Kiwon Lafiya
 • Osagie Ehanire (Edo) - Karamin Minista, Kiwon Lafiya
 • Audu Ogbeh (Benue) - Noma
 • Heineken Lokpobiri (Bayelsa) - Karamin Minista, Noma
 • Udo Udo Udoma (Akwa Ibom) - Kasafin Kudi Da Tsare-Tsaren Kasa
 • Zainab Ahmed (Kaduna) - Karamar Minista, Kasafin Kudi
 • Lai Mohammed (Kwara) - Yada Labarai
 • Amina Mohammed (Gombe) - Muhalli
 • Ibrahim Usman Jibril (Nasarawa) - Karamin Minista, Muhalli
 • Adamu Adamu (Bauchi) - Ilmi
 • Anthony Onwuka (Imo) - Karamin Minista, Ilmi
 • Muhammadu Bello (Adamawa) - Babban Birnin Tarayya Abuja
 • Okechukwu Enelamah (Abia) - Masana'antu, Cinikayya da Zuba Jari
 • Aisha Abubakar (Sokoto) - Karamar Minista, Masana'antu, Cinikayya da Zuba Jari
 • Mansur Dan-Ali (Zamfara) - Tsaro
 • Usani Usani Uguru (Cross River) - Niger Delta
 • Claudius Daramola (Ondo) - Karamin Ministan Niger Delta
 • Adebayo Shittu (Oyo) - Sadarwa
XS
SM
MD
LG