Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Binne Janar Attahiru, Sauran Sojojin Da Suka Mutu a Hatsarin Jirgi


Lokacin da ake shirin binne sojojin da suka mutu a hatsarin jirgin sama (Twitter/Nigerian Army)
Lokacin da ake shirin binne sojojin da suka mutu a hatsarin jirgin sama (Twitter/Nigerian Army)

An ga da yawa daga cikin iyalan mamatan mata da maza suna kuka yayin da suka kusanci motocin da aka dakko gawarwakin.

An gudanar da jana’izar babban hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a Abuja, da sauran sojojin da suka mutu a hatsarin jirgin sama da ya auku a Kaduna.

Attahiru ya rasu a ranar Juma’a tare da wasu sojoji 10 cikin har da janar-janar, a lokacin da jirginsu ya fadi a kusa da filin tashin jirage na kasa da kasa da ke Kaduna.

An gudanar da jan’izar ce da tsakar ranar Asabar agogon Najeriya a makarbartar sojoji da ke Abuja, bayan da aka yi masa sallah a babban Masallaci na kasa da ke birnin tare da biyar daga cikin sojojin wadanda Musulmai ne.

Akwatunan gawarwakin sojojin da suka mutu (Twitter/ Nigerian Army)
Akwatunan gawarwakin sojojin da suka mutu (Twitter/ Nigerian Army)

Daga cikinsu akwai mai tsaron lafiyar Attahiru, Manjo Lawal Hayat.

Wata sanarwa da kakakin sojan Najeriya Brig. Gen. Mohammed Yerima ya fitar, ta ce, a babbar Mujami’ar Abuja aka yi jana’izar wadanda mabiya addinin Kirista ne, cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su.

Karin bayani akan: Janar Ibrahim Attahiru, sojoji, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Daga baya an kai su makabartar sojojin, aka yi jana’izarsu baki daya su 11.

Jana’izar ta samu halartar jami’an gwamnatin Najeriya, gwamnoni da kuma shugabannin majalisar dokoki.

Wasu daga cikin iyalan mamatan a wajen jana'iza a Abuja (Twitter/Nigerian Army)
Wasu daga cikin iyalan mamatan a wajen jana'iza a Abuja (Twitter/Nigerian Army)

Hakazalika, iyalai, ‘yan uwa da abokan mamatan, sun samu halartar sallar jana’izar.

Gabanin a sallaci mamatan, an ba iyalansu dama don su yi ban-kwana tare da yi masu addu’a, lamarin da ya gudana cikin yanayi mai cike da juyayi da sosa rai.

An ga da yawa daga cikin iyalan mamatan mata da maza suna kuka yayin da suka kusanci motocin da aka dakko gawarwakin.

Hatsarin ya auku ne yayin da tawagar sojojin ke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja da misalin karfe shida na yammar ranar Juma’a a cewar sojojin Najeriya.

Rundunar sojojin Najeriya ta ce tana kan bincike don gano musabbabin wannan hatsari, wanda shi ne na kusan uku da ya rutsa da jiragen sojin kasar a wannan shekara.

Jami'an gwamnatin da suka halarci wajen jana'izar (Twitter/Nigerian Army)
Jami'an gwamnatin da suka halarci wajen jana'izar (Twitter/Nigerian Army)

A watan Fabrairun bana, wani jirgin sojin saman kasar ya fadi a yankin Abuja, dauke da sojoji bakwai – dukkaninsu sun mutu.

Sannan a watan Afrilu, wani jirgin saman sojin kasar da ke kai wa dakarun kasa dauki a yaki da mayakan Boko Haram, ya yi batan dabo.

Boko Haram ta yi ikirarin ita ta kakkabo jirgin wanda ke dauke da matuka biyu, amma rundunar sojin Najeriyar ta musanta ikirarin kungiyar.

A ranar 10 ga watan Agustan shekarar 1966 aka haifi Janar Ibrahim Attahiru a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

An Gudanar da Jana’izar Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:47 0:00

XS
SM
MD
LG