Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutuwar Attahiru Za Ta Mayar Da Hannun Agogo Baya - Buhari


Lokacin da shugaba Buhari yake yi wa Janar Attahiru Kwalliyar karin mukamin a fadarsa (Twitter/@NGRPresidency)
Lokacin da shugaba Buhari yake yi wa Janar Attahiru Kwalliyar karin mukamin a fadarsa (Twitter/@NGRPresidency)

A watan Janairu, Buhari ya nada Janar Attahiru, wanda ya gaji Janar Tukur Buratai tare da sauran hafsoshin sojojin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kwatanta rasuwar babban hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a matsayin wani abu da zai haifar da koma baya ga kasar.

Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a sa’o’i bayan rasuwarsa.

Janar Ibrahim Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgi da ya auku a kusa da filin tashin jirage da ke Kaduna a arewa maso yammacin kasar.

Jirgin ya taso ne daga Abuja zuwa Kaduna a cewar wata sanarwa da rundunar sojin Najeriyar ta fitar.

Lokacin da Ministan tsaron Najeriya ya je yi wa Buhari bayani kan hatsarin jirgin (Twitter/@BashirAhmaaad)
Lokacin da Ministan tsaron Najeriya ya je yi wa Buhari bayani kan hatsarin jirgin (Twitter/@BashirAhmaaad)

“Hadarin jirgin, ya yi mana kwaf daya a makasa, a kuma daidai lokacin da dakarunmu suka samo bakin zaren kawo karshen matsalar rashin tsaro da kasar ke fuskanta.” Muhammadu Buhari ya ce a sanarwa ta Shehu wacce ya wallafa a shafin Twitter.

Buhari wanda ya yi addu’a ga mamatan, ya sha alwashin ba za a manta da irin saudakarwar da suka yi ba.

Karin bayani akan: Janar Ibrahim Attahiru, Boko Haram, sojoji, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A daren ranar Juma'a ministan tsaron kasa Janar Bashir Salihi Magashi (rtd) ya je fadar Buhari ya yi masa karin bayanin kan hatsarin.

A watan Janairu, Buhari ya nada Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya gaji Janar Tukur Buratai tare da sauran hafsoshin sojojin kasar.

Wannan shi ne karo na uku a wannan shekara da jirgin sojin Najeriya ke yin hatsari ko ya bata a neme shi a rasa.

Lokacin da ministan tsaron Najeriya yake yi wa Shugaba Buhari kan hadarin jirgin (Twitter/@BashirAhmaad)
Lokacin da ministan tsaron Najeriya yake yi wa Shugaba Buhari kan hadarin jirgin (Twitter/@BashirAhmaad)

A halin da ake ciki fadar shugaban kasar, ta fitar da sunayen mutum 11 da suka mutu a hatsarin jirgin:

- Lt Gen. I. Attahiru

- Brig Gen. MI Abdulkadir

- Brig Gen. Olayinka

- Maj. LA Hayat

- Maj. Hamza

- SGT Umar

Matuka Jirgin Da Masu Hidima

- FLT LT TO Asaniyi

- FLT LT AA Olufade

- ACM Oyedepo

XS
SM
MD
LG