Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Gwamnoni Su Biya Basukan Da Aka Basu


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kafa wani Kwamitin bincike da zai bi sawun wasu makudan kudaden bashi da Gwamnatocin jihohi 35 su ka ci daga asusun Gwamnatin tarayya da sunan tallafi, wanda aka fi sani da “BAIL OUT” a Turance.

A wata sanarwa da Ministar Ma'aikatar Kudi Zainab Shamsunah Ahmed ta fitar ta ce ko wace jiha daga cikin jihohin nan 35 za ta biya Naira biliyan 17 da rabi. Don haka Majalisar Tattalin arzikin kasa ta amince da kafa kwamitin da ya kunshi Kungiyar Gwamnoni da Ma'aikatar Kudi da kuma Babban Bankin Najeriya. Ministan kudin ta ce Jihar Lagos ce kadai ba ta karbi bashin ba.

Masanin tattalin arzikin kasa da kasa Yusha’u Aliyu ya ce tuntuni ya kamata a fitar da tsarin biyan wadannan kudade, ganin cewa wasu gwamnonin sun kammala wa'adinsu, wasu kuma sun sauka sannan wasu yanzu ne ma za su shiga zabe a karo na biyu. Ya ce sai fa gwamnatin tarrayya ta dage sannan ta samu wadannan kudade.

Amma mai fashin baki a al'amuran yau da kullum kuma kwararre a fannin zamantakewar dan Adam daga Jihar Jigawa, Umar Faruk Wada ya ce lallai ne gwamnoni su biya wadannan basuka saboda ita kanta Gwamnatin Tarrayyya tana da bukatu irin na tsaro da gina kasa da ya kamata ta yi da wadannan kudaden.

Ya ce hasali ma yawancin gwamnonin ba su yi amfani da kudaden yadda ya kamata ba, domin wasu har yau ba sa biyan ma'aikata albashi mafi karanci wanda ya kama dubu 18 ne kawai. Faruk ya ce tsofaffin ma'akata da suka bar aiki ma har yau wasu ba a biya su fansho ba.

Ministar Kudi Zainab Shamsunah Ahmed ta nanata muhimmancin karkata akalar tattalin arzikin Najeriya daga man fetur zuwa wasu harkokin da za su kara mata adadin kudaden shiga.

Medina Dauda daga Abuja ta aiko mana da wannan rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG