Accessibility links

An Bullo da Wani Maganin Korar Sauro Mai Aminci


Sauro da yake kawo ciwon zazzabi

A yawancin sassan duniya, sauro na zuwa ne lokaci-lokaci. A wasu sassan kuma, sauro na dauke da munanan cututtuka kamar su zazzabin cizon sauro.

A yawancin sassan duniya, sauro na zuwa ne lokaci-lokaci. A wasu sassan kuma, sauro na dauke da munanan cututtuka kamar su zazzabin cizon sauro.

Kungiyar lafiya ta duniya ta kiyasta cewa kimanin mutane 630,000 suka mutu sakamakon cututtuka dangin su zazzabin cizon sauro a shekara ta 2012, yawanci daga kasashen Afrika kudu da Sahara. A yanzu, wata kungiyar masana kimiya daga Amurka suna aiki domin kawo wani magani wanda ke da inganci fiye da wadanda ake amfani da su yanzu kuma mara tsada domin korar sauro.

Binciken da ake gudanarwa a Jami’ar California Riverside, domin ya na dogarone da sanin cewa sauro yana amfani da abin sunsuna iskear da wuke hurowa daga lumfashinmu wanda kuma wannan abin sunsunen ne yake yin amfani da shi domin jin warin jikin mu yayinda ya zo kusa da mu.

Jagoran wannan bincike, Anandasankar Ray, yace masu kimiyya sun gwada fiye da sunadori miliyan guda kafin suka sami wani sunadari mai suna Ethyl Pyruvate wanda yake toshe wannan masunsunin na sauro.

“Yayinda muka shafa Ethyl pyruvate a hannun mutane muka kuma kai hannun jikin kejin sauro mayunwata, sauro kadan ne ke zuwa wajen hannun domin kadan daga cikinsu ne kadai suke iya jin warin hannun.” inji Ray.

Wani wanda yake cikin kungiyar masu binciken mai suna Genevieve Tauxe yace gano na’urar da sauron yake amfani da ita domin jin warin jikin mutum bai zama da sauki ba.

“Da wadannan kayan aikin, mun iya sa wata na’ura cikin hancin sauron, daidai wurin da yake amfani da shi wajen jin wari,” inji Tauxe.

Da wadannan kayan aiki ne, masanan kimiyya suka iya gane irin sadarwar da hancin sauro yake aikawa zuwa kwakwalwar sauron idan ya ji irin warin da yake so. Alamu a na’ura mai kwakwalma yana nuna lokacin da sadarwar ke da karfi da kuma lokacin da ba ta da karfi.

Ray yace magani dake kunshi da Ethyl pyruvate zai iya zama da saukin kudi fiye da wanda ke kunshe da DEET, wanda aka fi amfani da shi yanzu. Yace maganin dake kunshi da DEET yayi wa yawancin mutanen dake zama a yankunan da zazzabin cizon sauro yafi yawa tsada.

“Mai yiwuwa ta idan aka iya samun irin warin da sauron yafi amincewa da shi, za’a iya inganta DEET wanda kuma zai kai mu ga samun maganin da zai zama da taimako,” in ji shi.

Masanan kimiyya na Jami’ar California sun ce sun tabbatar cewa nan ba da dadewa ba zasu iya fitar da maganin sauro mai sauki da yaki sosai kan samai kuma inganci.
XS
SM
MD
LG