Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Mutane 23 a Samamen Faransa


Lokaci da ake kame a Faransa bayan hairn da ya halaka mutane 129

Hukumomin Faransa sun damke mutane 23 a jerin samamen da 'yan sanda su ka kai fadin kasar bayan harin ta'addancin da aka kai birnin Paris ranar Jumma'a, a daidai lokacin da hukumomi ke cewa sun gano mutumin da ya tsara munanan hare-haren.

An ce wani dan kasar Belgiam dan asalin kasar Morocco mai suna Abdelhamid Abaaoud, da alamar shi ya jagoranci shirin kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 129.

Hukumomin kasar Belgiam sun yi farautar Abaaoud a farkon wannan shekarar dangane da wani harin ta'addancin da aka kai kan 'yan sanda.

A kasar Faransa kuma Ministan Cikin, Gida Bernard Cazeneuve, ya fadi yau Litinin cewa an kai jerin samamen 'yan sanda wajen 170 da dare.

Baya ga wadanda aka damke, an kuma yi ma wasu daurin talala a gida.

An kai samamen ne da asubahin yau Litini a Toulouse, da Grenoble, da Jeumont, da Lyon da Bobigny da ke bayan garin Paris, wanda ya kai ga kama mutane sama da 10 da kuma kwace makamai masu yawa, ciki har da abin harba makamin roka, da bindigar kalashnikov da kuma rigar kariya da ake kira vest da harshen turanci.

Valls ya ce Faransa ta kau da hare-hare da dama, amma kuma ana iya fuskantar karin hare-hare cikin kwanaki ko makwanni masu zuwa.

XS
SM
MD
LG