Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Mutane Hudu Dake Shirin Kai Harin Ta'addanci a Australia


Jami'an tsaron Austrialia
Jami'an tsaron Austrialia

Jami'an Tsaron Australia sun dakile wani shirin 'yan ta'adda na harbo jiragen sama a kasar.

Firaministan Australia Malcolm Turnbull ya ce 'yan sandan kasar sun bankado wani shirin 'yan ta'adda na kakkabo wani jirgin sama.

Da ya ke bayani ga manema labarai a jiya Lahdi, Turnbull ya ce shi abinda ya fi bai wa muhimmanci da kuma abin da gwamnatinsa ita ma ta fi ba shi muhimmanci shi ne kare lafiyar 'yan Austarlia.

"Hadin kai da kuma aiki tare da jami'an leken asirin tsaron kasarmu da kuma jami'an tsaronmu, shi ne ginshikin kare 'yan Australia daga 'yan ta'adda. Hakika abu na farko ga gwamnati na da kuma gareni shi kare 'yan Australia. A kowace rana da kuma kowace sa'a, mu na masu tabbatar da cewa kariyarmu daga 'yan ta'adda na dada ingantuwa. Hadin kanmu na dada karuwa fiye da na baya. Yadda mu ke musayar bayanai ya fi na baya sauri."

Kwamishinan 'yan sandan Australia Andrew Colvin ya ce an damke mutane hudu, yayin da su ke kokarin shirya aikin ta'addanci, ta wajen amfani da bam hadin gida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG