Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahakan Ma'adanan Chile


Gugar ceto mahakan ma'adanan kenan zagaye da masu aikin ceton

Masu aikin ceto a kasar Chile na kan aikin kubutar da mahakan ma’adanai 33 din da su ka makale cikin wani ramin da ya rufta

Daya bayan daya, masu aikin ceto a kasar Chile ke ta kubutar da mahakan ma’adanai 33 din da su ka makale cikin wani rami mai zurfin fiye da rabin kilomita guda na tsawon fiye da watanni biyu.

Florencio Avalos dan shekara 31, shi ne na farko da aka ceto yan mintoci bayan karfe 12 na daren wurin, a yau dinnan Laraba, a cikin wata gugar karfe mai suna Phoenix. Ya sanya wani bakin tabarau don kare idonsa daga haske, bayan makwanni 10 din da ya yi cikin duhu. Avalos dai ya rungumi iyalansa da shugaban Chile, Sebastian Pinera.

Sannan sai aka sake zura gugar da wani likita a cikin ta. Aka sake zakulo dan hakar ma’adanai na biyu, mai suna Mario Sepulveda, wanda matarsa ta tarbe shi.

Gugar ta kan yi tsawon minti 15 kafin ta iso da mahakan ma’adanan daga ramin, mai zurfin mita 622. Ana ganin za a kai kwanaki biyu kafin a kammala ceto mutanen.

Za a tura jimlar masu aikin ceto a kalla hudu zuwa cikin ramin don taimakawa mahakan ma’adanan. Kuma in an ciro su nan da nan za a rinka yin masu jinya.

Yan jarida sama da 1000 ne dai suka yi cincirindo a wannan wurin da ke hamadar Chile, kuma ana yada aikin ceton kai tsaye a gidan talabijin din gwamnatin Chile.

Mahaka ma’adanan 33----32 yan Chile daya kuma dan Bolivia----sun kasance a makale na tsawon kwanaki 69, a wani yanayi na zafi, da gumi tun bayan ruftawar ramin da su ke ciki.

XS
SM
MD
LG