Accessibility links

An Cigaba Da Zanga-zangar Cibok a Duniya


An gudanar da zanga-zanga yau talata 6/5/2014 a kofar ofishin jakadancin najeriya dake Washington, DC, kan neman da a ceto dalibai mata na Chibok da 'yan Boko Haram suka sace

Jama’a da dama daga sassa na duniya, musamman ma Najeriya da Amurka suna kira da duniya akan ta tuba lamarin dalibannan, wadanda ‘yan kungiyar da ake cewa Boko Haram suka ce sun kama.

Suna kira “a dawo mana da yaranmu mata,” daruruwan mutane ne suka fito akan manyan titunan Amurka domin hankulan jama’a su koma kan wadannan dalibai.

“A tunanina, yana da matukar muhimmanci ga kowa da kowa, a bayar da tallafin kiran duniya ta lura da wannan lamari, kuma muna kara cigaba, shuwagabannin manyan duniya zasu lura, to hakan yasa akwai amfanin cigaba da wannan kiraye-kiraye,” inji Ama Owusu, wata jami’ar shirya gangami.

“Jama’a a duk fadin duniya suna tattauna wannan batu saboda wannan keta hakkin bil adama ne, a lokacin da wadannan yara mata suke neman ilimi, domin taimakawa suma a duniya,” a cewar Ratibah El-Gazzear, mai shirya gangami.

Wannan satar dalibai yara mata masu shekaru daga 15 zuwa 18 ya baiwa mutanen Najeriya mamaki, kuma hakan ya bayyana irin rashin doka da odar da ta’addanci da akeyi a wannan waje mai talauci da zafi, kuma ya kasha daruruwan mutane a lokutan baya.

Masu zanga-zangar sunyi makakin da suka ga an rufe haraba ta biyu da suka tanada, idan ta farko ta samu tangarda, ba tare da wani bayani ba.

“Mu… babu yadda za’a hana mu, ta kowace hanya. Maganar gaskiya, hakan ne ma zai saka mu kara zage damste a gwagwarmayarmu. A wajen, na lokaci mai tsawo bamu ga dauki wani kyakyawan mataki ba game da ceto wadannan dalibai ba. Zamu cigaba da zanga-zanga na lokaci mai tsawo, zamu jure zama, duk inda aka rufe, zamu samu wani wajen na daban. Yanzu muna zaune ne a gefen titi, kuma a nan zamu cigaba da zama, muna tattanawa da gudanar da shawarwari,” a cewar Hadiza Bala Usman, daya daga cikin masu shirya zanga-zangar “A Dawo Mana Da Yaranmu Mata”, ko “Bring Back Our Girls” da turancin Ingilishi.

Dino Melaye, tsohuwar ‘yar Majalisar Wakilan Tarayya ce, kuma tana daga cikin shugabannin kungiyar yaki da cin hanci da rashawa, itama ta dauki alwashin cigaba da zanga-zanga har sai an nemo daliban.

An cigaba da zanga-zanga duk da cewa an rufe babban Birnin Tarayyar ruf, saboda dalilan tsaro.

Kasar Faransa ce ta karshe ta da mika hannun tallafi ga Najeriya Larabannan, tana cewa zata kara karfafa mutuntakar bayanan sirri da Najeriya, da kuma aiki jami’an tsaro domin takalar Boko Haram, kungiyar ‘yan bindigan da ta dauki alhakin harin.
XS
SM
MD
LG