Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

​An Kara Sace Yara Mata


Rahotanni dake zuwa daga arewa maso gabashin Najeriya sunce ‘yan bindiga cikin dare sun kara sace mata 8 wadanda shekarusu suka kama daga 12 zuwa 15 a garin Warabe, a karamar Hukumar Gwoza dake jihar Borno.

Jami’an Tsaro da mazauna garin sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindiga sun kwashe wadannan yara mata suka zuba su a mota, a ciki harda dabbobi da kayan masarufi wadanda duk suka sata.

Ya zuwa yanzu ba’a san inda suka tafi da yaranba.

Wannan shine karo na biyu da ‘yan bindiga suke sace mata kananan yara a arewa maso gabashin Najeriya cikin makonni uku. A kwanakin baya, ‘yan bindiga sun sace dalibai mata sama da 200 a makarantar sakandare dake Cibok a Jihar Borno, lamarin da iyaye suke cewa gwamnati tayi wa batun rikon sakainar kashi, saboda rashin bin sawun yaran.

Yanzu dai Najeriya da wasu sassa na duniya ana zanga-zangar lumana domin kira ga hukomomi akan su kara himma wajen neman daliban.

‘Yan majalisun dokokin Jihar Borno sun zargi da hannun shugaba Jonathan a sace daliban, irin zargin da Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako yayi a kwanakin baya. Gwamnatin Tarayya ta karyata zargin Murtala Nyako.

Bayanai dake fitowa da Najeriya na nuna cewa akwai rashin jituwa tsakanin gwamnan na Jihar Borno da Shugaba Jonathan game da yadda ake tafiyar da yaki da ta’addanci a Jihar.

Labarai masu alaka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG