Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cika Shekaru 100 Tun Yakin Duniya Na Daya


shekaru 100 bayan yakin duniya na daya -- shugabannin kasashe 70 su ka taru a dandalin Arc de Triomphe na kasar Faransa don tunawa da miliyoyin mutanen da su ka mutu a yakin.

Shugaban Amurka da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sune shugabanni biyu na karshe da suka isa wurin bukin.

A jawabinsa, Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi Magana a kan sadaukar da rayuka da aka yi shekaru da dama da su ka gabata, a yakin da aka shafe shekaru hudu ana yi a Turai. Ya ce "Alfahari da kasa akasin Kishin kasa ne."

Yace tsofaffin miyagun dabi’un da aka yi fama da su a baya, suna shirin shuka rudani da mutuwa” Wani lokaci tarihi yakan yi barazanar sake bayyana ya yi kokarin maida hannun agogo baya a zaman lafiyar da muke zaton mun samu ta dalilin zubar da jinin kakanninmu.

Daga baya jiya lahadi, Macron ya jagorancin wani dandalin wanzar da zaman lafiya da shugabar kasar Jamus Angela Merkel tace an yi ne da nufin nuna irin kokarin da ake yi na kara samun zaman lafiya a kasashen duniya ko da yake har yanzu akwai aiki tukuru a gabanmu.

Shugaba Trump, mai yayata akidar Kishin kasa da fifita Amurka bai halarci taron ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG