Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Wuka Ya Halaka Mutum Daya a Australia


Emergency rescue personnel near the Bourke Street mall in central Melbourne, Australia, November 9, 2018.
Emergency rescue personnel near the Bourke Street mall in central Melbourne, Australia, November 9, 2018.

Wani harin Ta'addanci da aka kai a garin Melbourne da ke Kasar Australia ya halaka mutun daya yayin da mutun uku suka jikkata.

A yau Juma’a ne wani mutum ya daba wa mutane da dama wuka, inda ya kashe mutun daya a garin Melbourne da ke Australia.

‘Yan sandar Kasar Australia sun ce sun yi imani harin da aka kai da wuka yau a garin na Melbourne, wanda shi ne birni na biyu mafi girma a kasar yana da alaka da ta’addanci.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Victoria, Graham Ashton ya ce wanda ake zargi da kai harin ya mutu, kuma dan asalin kasar Somaliya ne wanda 'yan sanda sun san shi sosai.

'Yan sanda sun bude wuta akan wanda ake zargin a lokacin da yake kokarin kai farmakin na wuka akan wasu ‘yan sanda guda biyu a cikin garin, kafin daya daga cikin 'yan sandar ya harbe shi a kirji, bayan nan ne aka dauke shi zuwa asibiti inda ya mutu daga baya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG