Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Zaman Majalisun Tarayyar Nigeria


Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Majalisar Dokokin Nigeria ta dage zaman ta Talata, sai shugabanninsu sun zauna kana su sa ranar da zasu koma zama

Mai magana da yawun majalisar wakilai Abdulrazak Namdas a wata hira ta musamman da ya yi da wani gidan talibijan mai zaman kansa dake Abuja.

Ya ce a da sun amince dawowa aiki Talata amma babu alamun hakan zai yiwu. Yace sai shugabannin majalisun sun zauna a nan gaba su tsayar da ranar komawa aiki.

A bangaren majalisar dattawa Sanata Abu Ibrahim yace bas hi da masaniyar bude Majalisar. Saboda duk kafofin da ake bi na sanar da su ko rubuce, ko ta text, shi bai gani ba.

Batun canza shugabancin majalisun, musamman majalisar dattawa shi ne mutane ke harsashe a kai wanda shugaban RAPC Buba Galadima ya yi tsokaci akai.

Yace ba zancen kudin da za’a baiwa INEC ne dalilin son a bude majalisar saboda wai INEC na da kudi da za ta yi anfani dashi har zuwa watan goma na aikace aikacen ta. Ya ce me ya sa tuntuni ba’a kudin INEC cikin kasafin kudi, sai yanzu da ake son a labe da INEC din a tsige shugaban majalisa? Yana cewa abun kunya ne kuma ba zai yiwu ba bisa doka.

A nashi nazarin Farfesa Jibrin Ibrahim na cibiyar habaka Dimokradiya ya ce abun da doka ta tanada shi ne ‘yan majalisa zasu taru su zabi wanda suke so ya jagorancesu. A yawancin lokacin idan suna zabe zasu zabi wani daga bangaren dake da rinjaye ne. Injishi, a cikin wannan halin na baraka da canza sheka ba’a san wanda yake da rinjaye ba.

Sai dai wai dawowar nada nasaba ne da bukatar da shugaban kasa ke da ita na neman ‘yan majalisar su sa hannu a wasu bukatu.

A saurari rahoton Medina Dauda

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG