Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dakatar Da Kanye West Daga Amfani Da Instagram


Kanye West, wanda ake kira Ye yanzu

An dakatar da Kanye West daga Instagram na tsawon sa'o'i 24 ne saboda keta manufofin dandalin kan kalaman ƙiyayya da cin zarafi,  in ji mai magana da yawun Meta Laraba.

Instagram ya cire tsokacin daga shafin mawakin saboda keta manufofin kuma ya hana shafin yin rubutu, yin tsokaci da aika saƙonni kai tsaye, da sauran ayyuka, na tsawon awanni 24 kammar yadda jaridar Huffpost ya rawaito.

Instagram sau da yawa yana sanya takunkumi a kan shafukan da ke karya dokokinsa kuma kamfanin na iya ɗaukar ƙarin matakai idan aka ci gaba da cin zarafi, a cewar mai magana da yawun Meta, wanda ya mallaki Instagram.

A cewar TMZ, an goge aƙalla tsokacin da yayi ɗaya daga shafin na West. A cikin sakon, ana zargin cewa ya yi amfani da kalaman wariyar launin fata da ya ke kwatanta mai gabatar da shirin "The Daily Show" Trevor Noah, wanda kwanan nan ya soki West saboda tursasa bazawararsa Kim Kardashian a bainar jama'a yayin da suke ci gaba da lamarin kashe aurensu.

West, wanda a hukumance ya canza sunansa zuwa Ye, ya yi ta ta da hankalin Kardashian da saurayinta, ɗan wasan barkwanci Pete Davidson, tare da fallasa cikakkun bayanai game da al'amuransu na sirri ga miliyoyin mabiyansa.

A farkon wannan watan, ya fitar da wani sabon faifan bidiyo na kiɗa wanda a cikin yak e cewa zai yanke kan Davidson tare da binne shi da rai.

- Hadiza Kyari ce ta fassara wannan labari wanda ya samo asali daga TMZ.

XS
SM
MD
LG