Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Daura Auren Yarima Harry da Meghan Markle


Britain Royal Wedding
Britain Royal Wedding

An daurawa Yariman Birtaniya Harry da Meghan Markle aure yau a garin Windsor dake bayan garin birnin London.

Yarima Charles, mahaifin Harry ya kama hannun amaryar ya rakata zuwa inda za a daura masu aure.

Tsohuwar ‘yar wasan fina finan ba-amurka tun farko ta bada tabbacin cewa, mahaifinta ba zai halarci bukin ba, sabili da rashin lafiya da yake fama dashi, ‘yan kwanaki bayanda aka rika bayyana kila-wakala kan ko zai je auren.

Mutane sunyi dafifi zuwa garin mai dumbin tarihi, yayinda masu fatar Alheri suka yi ta kokarin yin ido hudu da amarya da angon. Dubban jami’an ‘yan sanda sun gudanar da ayyukan tsaro mafi girma a cikin shekarun nan, da aka biya da kudin gwamnati abinda wadanda suke adawa da masarautar suka kushewa.

Masu goyon baya kuma sun bada hujjar cewa, yana yiwuwa baki da wadanda zasu kalli bukin a manyan akwatunan talabijin a duk fadin kasar zasu kashe kudi sosai.

Mutane dari shida aka gayyata su halarci bukin, galibi wadanda suke da alaka da ma’auratan.

An kuma gayyaci wadansu mutane dubu biyu da dari biyar su shiga harabar majami’ar da aka daura auren domin ganin shiga da fitar ango da amaryar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG