Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Daure wata Ba-Amurkiya a Zimbabwe Saboda Rashin Da'a ga Mugabe


Ba-Amurkiya Martha O'Donovan
Ba-Amurkiya Martha O'Donovan

Wata kotu a kasar Zimbabwe a jiya Asabar ta bada umarni daure wata yar asalin kasar Amurka a gidan yari yayin da ake tuhumarta da cin mutunci da nuna rashin da’a ga shugaba Robert Mugabe.

An kama yar kasar Amurkan mai suna Martha O’Donovan da take yiwa wani telbijin yanar gizo a kasar Zimbabwe aiki ne a ranar Juma’a, yayin da yan sanda suka je gidanta bayan sun samu izinin kamata daga kotu a wani samame da suka kai mata da sanyi safiya.

A jiya Asabar wata karamar kout ta mikata ga babban kotun kasar don bata beli yayin ake tuhumarta da laifin mataki na uku.

Obey Shava yana cikin kungiyar lauyoyin kare hakkin bil adama a Zimbabwe kuma shine lauyan yar Amurkan O’Donovan.

Lauyan yace zamu je babban kotun a ranar Litinin don neman izinin beli. Amma da farko mun je ne don mu kalubalanci kama wanda muke mata aikin. Mun nuna cewa yanda aka kamata ya sabawa tsarin dokokin kasar.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG