Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dinke Barakar Da Ta Kunno Kai a Fadar Sarkin Musulmi


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar

Manyan Sarakuna sun taka muhimiyar rawa a sasanta takaddamar da ta kunno kai a fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar.

Rahotannin daga birnin Shehu na cewa, an kawo karshen takaddamar da ta barke a Fadar Sarki Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar, bayan da aka samu sabani tsakanin Sarki Sa'ad da Magajin Garin Sokoto Alhaji Hassan Danbaba.

Bangarorin biyu sun sami matsala ne a 'yan kwanakin nan, lamarin da ya kai ga Alhaji Danbaba ya ajiye mukaminsa na Magajin Gari da ya kwashe shekaru 20 yana rike da shi.

Bayanai sun yi nuni da cewa, Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, wanda shi ma babban makusanci ne na daular ta Usmaniya na daya daga cikin sakarunan da suka shiga tsakani wajen ganin an sasanta wannan takaddama.

Sauran sarakunan da suka shiga tsakani a karkashin wani kwamiti da aka kafa domin sasanta rikicin sun hada da mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da Sarkin Sudan na Kontagora da Etsu Nupe.

Babu takamaiman bayanan da suka fito daga zaman da aka yi wajen sulhun wanda aka yi shi cikin sirri, amma dai alamu sun yi nuni da cewa sulhun ya ka kai ga gaci inda rahotanni suka nuna cewa, Alhaji Hassan Danbaban ya janye murabus din da ya yi tun farko.

Wata alama dake sake nuna tabbacin samun daidaito ita ce yadda aka ga Magajin Garin na Sokoto, ya halarci wasu manyan taruka biyu tare da mai alfarma Sarkin Musulmi a yau lahadi.

Domin jin karin bayani, saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG