Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Aikin Sake Kirga Kuri’u "Da Hannu" a Jihar Georgia a Zaben Amurka


Yadda ake sarrafa kuri'u a Atlanta, Georgia
Yadda ake sarrafa kuri'u a Atlanta, Georgia

Jami’an zabe a jihar Georgia da ke Amurka sun fara aikin sake kidaya kuri’un da aka kada a sassan jihar 159 a zaben shugaban kasar da aka yi a makon da ya gabata - amma wannan karon da hannu.

Doka ta tanadi cewa a sake kidaya kuri’un da hannu domin tabbatar da cewa na’ura ba ta yi kuskure ba, ba wai don ana zargin an samu tangarda da sakamakon zaben ba.

Sakataren Jihar ta Georgia, Brad Raffensperger ya zabi a sake kidaya kuri’un na zaben shugaban kasa ne saboda yadda aka kusan yin kankankan a sakamakon zaben jihar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Joe Biden na jam’iyyar Democrat na gaban shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican da kuri’a 14,000.

Hakan ya sa ake ganin ya zama dole a sake kirga kuri’un amma da hannu.

Ana sa ran da misalin karfe 11:59 na daren ranar Laraba za a kammala aikin sake kirga kuri’un a cewar AP.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG