Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Bada Takardun Bizar Shiga Saudiyar na Hajin Bana


Zulumin maniyyata aikin Hajin bana zai kwanta don fara bada itakardun biza.

Zulumin maniyyata aikin Hajin bana zai kwanta don fara bada izinin shiga Saudiyar daga ofishin jakadancin Saudiya din.

An samu jinkirin bada takardun biza da Saudin ta sanar cewa zata farawa tun makon jiya, wanda yasa zulumin, bamamakin maganar cutar Ebola, ce ta haddasa jinkirin.

Babban Likitan Alhazai Dr, Ibrahim kana, yace zasu tsaurara matakan binciken maniyyata, kafin basu izinin shiga jirgi.

Ya kara da cewa duk wanda aka samu da zazzabin to tabachi hakika bazai samu zuwa aikin Haji ba.

Saudiya, ta dakatar da kasashe uku, na Afirka ta yamma da suka fi fama da cutar daga aiki Hajin bana, wato Liberia, Guinea da Sierra Leone.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG