Accessibility links

An Fara Gudanar da Bukukuwan Cikar Shekaru 100 da Kafa Najeriya


Shugaba Goodluck Jonathan

Shugabannin kasashen Afirka kusan 30 su na halartar bukukuwan da ake yi a Abuja don karrama cikar shekaru 100 da kafa kasar

An fara gudanar da bukukuwan cikar shekaru 100 da kafa Najeriya a Abuja, inda a yau alhamis aka gudanar da taro kan tsaron lafgiyar jama'a, da zaman lafiya a kasa.

Shugabannin kasashen Afirka kusan 30 suke halartar bukukuwan da ake yi, inda a yau din suka yi ta gabatar da jawabai kan yadda za a iya samun wanzuwar zaman lafiya da kare hakkin al'umma.

A shekarar 1914, turawan mulkin mallaka na Ingila suka hada yankuna uku da sukewa mulkin mallaka dabam-dabam a lokacin, suka zamo kasa guda da suka sanya ma suna Najeriya. Yankunan sune Lardin Arewa, Lardin Kudu da kuma Lardin Lagos.

Wakilinmu Umar Faruk Musa ya aiko da cikakken bayani daga Abuja.

XS
SM
MD
LG