Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Kamfen Din Ceto Mutanen Da 'Yan Boko Haram Suka Sace A Nijar


Kaka Touda shugaban kungiyar rajin ganin an sako 'yan Nijar da Boko Haram ta sace

Kamar yadda 'yan Boko Haram suka sace 'yan matan makarantar sakandare ta mata dake Chibok, haka suka sace wasu yara da mata kimanin 39 a yankin Diffa cikin kasar Nijar lamarin da yanzu ya harzuka wasu suka tashi suka kaddamar da kamfen din ceto mutanen da aka sace

Mai magana da yawun 'yan rajin ganin an sako 'yan Nijar da Boko Haram ta sace, Kaka Touda, ya ce ranar 26 ga watan Satumbar bara 'yan Boko Haram sun sako biyu cikin mutanen da suka sace a Ngalewa, yankin Diffa, amma tun daga lokacin babu labarin sauran 37 dake hannunsu.

A cewarsa su 'yan Boko Haram sun yi bidiyo akan 'yan matan Chibok da suka sace domin duk duniya ta tabbatar sun sace su amma basu yi haka ba akan na Nijar da suka sace. Rashin sanin halin da sauran 37 ke ciki ya sa suka fito su soma fafutikar ganin an sako su.

Inji Kaka Touda zasu yi amfani da duk kafofin labarai har da na zamani su wayar da kawunan mutane akan lamarin, tare da kiran shugabanni su tashi tsaye akan lamarin. Ya kira shugabannin kasar da manyan mutane su soma magana akan wadanda aka sace kamar yadda kungiyar Bring Back Our Girls, BBOG, ta Najeriya keyi.

Akan cewa ba'a tunawa da mutanen saboda ba'a ambatarsu, Kaka ya ce sau daya shugaban kasa ya ambacesu a wani jawabi da ya yi inda ya umurni jami'an tsaro da su tabbatar sun zakulo mutanen da aka sace tare da wadanda suka yi aika aikar. A cewarsa yau kwanaki dari biyu ke nan da sace mutanen kuma babu labarinsu.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG