Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Kidayar Kuri'un Zaben Raba Gardama Na Afirka Ta Tsakiya


Kidayar kuri’un kada kuri’a ya fara a jiya Lahadi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a zaben raba gardamar da aka yi tsakanin tsoffin Firaministocin kasar.

Wadanda dukkansu suka yi alkawarin maido da zaman lafiya a rikicin da aka fi shekaru biyu ana yinsa tsakanin musulmi da kiristocin kasar.

Zaben na jiya ya hada da wanda zaben farko na 30 ga watan Disambar bara ya nuna shi yayi nasara wato Aniset Jojis Dologwil, wanda aka ce yaci da kason kuri’un 24 da kuma Faustin Acange Tiyodora da ya gama na barar da kason kuri’u 19.

Ya dai kamata ace an sake zaben tuntuni amma aka dinga dagewa har zuwa jiya da aka samu aka kada kuri’un raba gardamar.

Baya ga kuri’un zaben shugaban kasar, masu kada kuri’ar zun zarce ne da zaben ‘yan Majalisun kasar bayan watsi da na watan Disambar da aka yi.

An dai rurrushe zabukan bayan ne saboda suna cike da dimbinm kurakurai. Duk wanda aka bayyana cewa yaci zaben, to shine zai maye gurbin shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Wacce aka ta karbi jagoranci a shekarar 2014, shekara 1 bayan ‘yan tawayen Seleka sun hambarar da gwamnatin Fransuwa Bozize.

XS
SM
MD
LG