Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Samun Sakamakon Zaben Fitar Da Gwani Na Shugaban Kasa A Kasar Guinea


Tsohon firayim minista Cellou Dalein Diallo a dakin taro na Al'umma a Conakry, ranar 21 Satumba 2010.

Tsohon firayim minista Cellou Dallein Diallo yana gaban madugun hamayya Alpha Conde da rata kadan a sakamakon da aka fara samu daga wasu gundumomi

Sakamakon da aka fara samu daga zaben fitar da gwani na shugaban kasa a Guinea-Conkary ya nuna cewa tsohon firayim minista Cellou Dalein Diallo yana gaban madugun hamayya Alpha Conde, da 'yar karamar rata.

Sakamako daga gundumomi biyar da kuma wasu ofisoshin jakadancin Guinea 12 inda 'yan kasar dake zaune a can suka kada kuri'a, ya nuna Mr. Diallo yana kan gaba da kuri'un da ba su kai dubu 11 ba.

A yau laraba za a ci gaba da kidaya kuri'u.

Dakarun tsaro sun shiga cikin mutanen da suka taru a kofar ofisoshin zabe na gundumomin dake Conakry domin hana abkuwar irin fadan da ya barke a tsakanin magoya bayan 'yan takara dabam-dabam a kan tituna lokacin yakin neman zabe.

A makonnin da suka wuce kafin wannan zabe, magoya bayan 'yan takarar biyu sun yi ta bai wa hammata iska a Conakry da wasu biranen. 'Yan takarar biyu da kuma 'yan kallo sun roki al'ummar Guinea da su yi na'am da sakamakon zaben duk yadda ya kasance.

Mr. Diallo dai Bafulatani ne, kabilar da ta fi girma a kasar Guinea, yayin da Mr. Conde ya fito daga karamar kabilar Malinke.

XS
SM
MD
LG