Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Zata Tura Karin Sojojinta Zuwa Ivory Coast


Dan takara Alassane Ouattara yana kada kuri'arsa a Abidjan a zagayen farko na zaben shugaban kasa ranar 31 Oktoba, 2010

Za a tura sojojin ne daga rundunar majalisar dake Liberiya domin karfafa tsaro lokacin zaben shugaban kasa na fitar da gwani da za a yi ranar lahadi a kasar ta Ivory Coast

Majalisar Dinkin Duniya ta ce zata tura karin sojojin kiyaye zaman lafiya 500 daga Liberiya zuwa Ivory Coast ko Cote D’Ivoire, domin su taimaka wajen tabbatar da doka da oda a lokacin zaben fitar da gwani na shugaban kasa da za a yi ranar lahadi mai zuwa.

Jiya laraba dukkan wakilan Kwamitin Sulhun majalisar suka jefa kuri’ar bayar da iznin tura bataliyoyi uku da jiragen helkwafta biyu daga rundunar majalisar dake Liberiya.

Ana zaman tankiya sosai a kasar Cote D’Ivoire yayin da ake shirin zaben shugaban kasar na farko a bayan yakin basasa. Magoya bayan dan takarar hamayya Alassane Ouattara sun yi ta cacar-baki da masu goyon bayan shugaba Laurent Gbagbo.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga sassan da su kai zuciya nesa.

Tsohon shugaba Henri Konan Bedie yana jefa kuri'arsa a zagayen farko na zaben
Tsohon shugaba Henri Konan Bedie yana jefa kuri'arsa a zagayen farko na zaben

Tun da fari a jiya laraba, Tarayyar Turai ta zargi hukumar zabe ta kasar Cote D’Ivoire da laifin hana ‘yan kallonta sukunin ganin kwakwaf game da wannan zabe da ake shiryawa. Jami’an Cote D’Ivoire ba su ce uffan kan wannan zargin ba.

Samun nasara a zaben fitar da gwanin zai dogara a kan shawo kan kashi 25 cikin 100 na masu jefa kuri’ar da suka zabi mutumin da ya zo na uku a zagayen farko, tsohon shugaba Henri Konan Bedie. Mr. Bedie dai ya ayyana goyonb bayansa ga Alassane Ouattara.

XS
SM
MD
LG