Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Yaki da Zarmiya Ta Kasa da Kasa, Transparency International Tace Nahiyar Afirka ce Yankin Da aka Fi Kowanne Cin Hanci Da Rashawa A Fadin Duniya


Taswirar Duniya inda Kungiyar Transparency mai yaki da zarmiya take nuna inda ake da matsalar a fadin Duniya.

Somaliya ce take kan gaba a jerin kasashen,cikin rahoton kungiyar na shekara shekara, da ta sake talatan nan. Kungiyar ta auna mizanin cin hanci da rashawa cikin kasashe 178.

Wata Kungiyar kasa da kasa mai yaki da zarmiya tace nahiyar Afirka ce yanki da aka fi cin hanci da rashawa a fadin Duniya,inda Somaliya take kan gaba.

Talatan ce kungiyar Transparency International, ta saki rahotunta na shekara shekara,inda ta yi nazarin alamun cin hanci da rashawa a kasashe 178. Rahoton na bana ya jera kasashen Afirka shida cikin kasashe 10 da suka dara saura a Duniya wajen cin hanci da rashawa.

Kasashen sune Somalia,Sudan,Cadi,Burundi,Angola,da kuma Equatorial Guinea. Kungiyar tana auna ta wajen baiwa kasashe maki 10,sifiri shine alamar kasa data kure sikeli, a cin hanci d a rashawa.

Kasashen Afirka 44 cikin 47 da kungiyar ta auna sun sami kasa da maki biyar, hakan yana nufin suna da mummunar matsalar cin hanci rashawa.

Kungiyar mai skatariyat a Berlin,yace kasar Botswana ce a nahiyar Afirka inda ba'a tabka cin hanci rashawa kamar saura.

XS
SM
MD
LG