A wannan zama wanda shine na farko tunda gwamnati ta daukaka kara a kan hukumcin wata babbar kotun kasar ta bayar da umarni a saki shugaban kungiyar shugaban ‘Yan Shi’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, an kwashi lokaci ana tada jijiyar wuya tare da musayar yawu tsakanin lauya mai kare El-Zakzaky Femi Falana, da lauyan gwamnati Oyi Kolawusho.
Femi Falana ya kalubalanci bukatar lauyan gwamnati wanda ya nemi a gyara wadansu takardu da suka shafi karar da suka daukaka. Femi Falana yace bai zai yiwu gwamnati tazo da wata bukata ba a yanzu, bayan taki bin umarnin babbar kotun tarayya a hukumcin da ta bayar a can baya.
Yace wannan kotun bata da hurumin sauraron wannan kara da gwamnati ta daukaka sai an saki Sheik El-Zakzaky
Duk da rashin samun bayanai daga bakin gwamnati, alkalan daukaka karar, sunce sakin El-Zazzaky ba zai hana gwamnati daukaka kara ba
Ga cikakken rahoton Madina Dauda.
Facebook Forum