Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zabe A Najeriya


Masu zabe a mazabar Hotoron Arewa a Kano su na jiran a tantance su kafin su fara jefa kuri'unsu

Asabar,‘Yan Najeriya sun tafi rumfunan zabe, domin su zabi wakilan majalisar dokokin kasar,cikin matsanancin matakan tsaro,bayan wata fashewa a wani ofishin hokumar zabe.

Asabar,‘Yan Najeriya sun tafi rumfunan zabe, domin su zabi wakilan majalisar dokokin kasar,cikin matsanancin matakan tsaro,bayan wata fashewa a wani ofishin hokumar zabe.

Wata fashewa a ofishin hukumar zabe a yammacin jiya jumma’a kusa da babban birnin kasar Abuja,ya halaka akalla mutane takwas. Wasu da dama kuma suka jikkata a fashewar da ta auku a Suleja. Kamfanin dillancin labaran faransa ya bada labarin cewa an dage zabe a Suleja.

Sau biyu Najeriya tan adage zaben shiga majalisar dokokin kasa.An soke zaben a makon jiya domin karancin kayan zabe.

A jihar Borno,Yansanda sunce ‘yan bindiga sun harbe suka kashe mutum hudu a yammacin jiya jumma,a yayinda suke shirin karbar kayan zabe. ‘Yansanda suka ce daya daga cikin wadanda aka kashe wani kusa ne na jam’iyyar PDP mai mulkin kasar.

Najeriya ta dauki karin matakan tsaro gabannin zaben na yau,ma’aikatar harkokin cikin gida ta rufe dukkan kan iyakokinta,yayinda rundunar ‘yansanda ta tura karin jami’ai domin sintiri kan tituna,suna takaita zirga zirgar motoci. Sojoji kuma suna sa ido a wuraren zabe.

XS
SM
MD
LG