Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar dake mulkin Nigeria PDP na samun koma baya a zaben majalisun Tarayya


Dan Nigeria ke karanta jaridar dake dauke da kanun tada bom da ya halaka wata mace jami'ar 'yan sanda da kuma wasu mutanen su 10 a Abekuta, Nigeria. Gungun jami'an kallo, ke bayyana cewar zagayen farko daga cikin zagaye ukun zaben da za'a yi a Nigeria n
Dan Nigeria ke karanta jaridar dake dauke da kanun tada bom da ya halaka wata mace jami'ar 'yan sanda da kuma wasu mutanen su 10 a Abekuta, Nigeria. Gungun jami'an kallo, ke bayyana cewar zagayen farko daga cikin zagaye ukun zaben da za'a yi a Nigeria n

Bisa ga kwarya-kwaryar sakamakon farkon da aka samu, jam’iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta rasa rinjayen da take dashi a majalisun tarayya.Duk da haka dai kwarya-kwaryar sakamakon zaben na ranar Aasabar ya nuna jam’iyyar ta PDP tana sahun gaban sauran jam’iyyun da suka tsaida’yan takara a zaben majalisar dattawa da ta wakilai, amma babu wata tazara mai yawa.

Kididdigar rabin yawan kuri’un da jam’iyyu suka samu ta nuna jam’iyyar hamayya ta (ACN) tayi ba zata a samun yawan kujeru a yankin Kudu Maso Yammacin Nigeria. Kazalika ita ma jam’iyyar (CPC) tayi rawan gania jihohin Arewa. Jam’iyyar CPC Karkashin inuwarta ce tsohon shugaban Gwamnatin mulkin sojin Nigeria Muhammadu Buhari zai yi takarar shugaban kasa, ana kuma kyautata cewar shine a sahun gaban masu tinkarar shugaba mai ci Goodluck Jonathan a zaben Asabar mai zuwa.

Jami’an kallo na kungiyar Tarayyar Turai, ran litinin suka bada sanarwar cewa zaben Asabar da ta gabata anyi shi cikin yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali, hakan kuma yana karfafa gwiwar kasa da kasa An sami nasarar gudanar dazaben duk da barazanar tada bom da aka yi a Suleja da Maiduri. An dage gudanar da zaben har sau biyu saboda rashin isar kayan aiki wuraren zaben dake gunduma da majalisun kananan hukumomin Nigeria.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG