Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Neja Kai


Nigerian soldiers (File photo)

Mun sami rahoton fashwewar wani abinda ake zaton bam ne ya tashi a garin Suleja na jihar Neja.

Mun sami rahoton fashwewar wani abinda ake zaton bam ne ya tashi a garin Suleja na jihar Neja, yayinda ake saura kwana daya al'ummar Nigeria su fito wajen jefa kuri'unsu a zaben 'yanmajalisun dokoki na tarayya. Rahottanin sunce bam din ya hallaka mutane da yawa, ya raunana wasu da yawa sannan kuma ya tarwatsa opishin Hukumar zabe (INEC) dake garin na Suleja. Wani shedu mai suna Yakubu Adamu ya gaya wa Sashen Hausa na VOA cewa ya ga mutane da yawa ana kawo su assibitin Suleja jina-jina, cikin rudami. A yanzu haka dai hukumomi na gudanar da binciken abinda ya faru. Za'a iya tuna cewa makamancin wannan bam din ya tashi a makkonin baya a nan Suleja yayinda ake tarukkan kyamfen din wasu 'yan takaran majalisar dattawa na jihar. A wancan lokaci, kamar mutane 10 suka rasa rayukkansu, da dama suka ji rauni. Gwamnan jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu na wurin da wancan bam din ya tashi, amma dai bai ji rauni ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG