Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zaman Tabbatar Da Amy Coney Barret A Matsayin Alkalin Kotun Kolin Amurka


Amy Coney Barret
Amy Coney Barret

A jiya Litinin ne aka fara sauraren bahasin tabbatar da Any Coney Barret wacce za a nada alkaliyar kotun kolin Amurka a Washington, inda Barrett ta fadawa majalisar dattawa cewa bakamata kotuna su shata tsari ba, kamata ya yi su bar wa shugabannin Amurka da majalisar dokoki.

Barrett ta gindaya wata tarjama mai tsauri a kan rawar da babbar kotu take takawa, tana mai cewa, ba an yi ta ne dan ta magance kowace matsala ba ko kuma ta gyara dukan kura kuran da aka tafka a rayuwar jama’a ba.

Yayin da aka fara sauraren, Sanata Dianne Feinstein mai jagorantar Democrat a kwamitin shari’a na majalisar dattawa, nan take ta nuna cewa marasa rinjayi na Democrat nada wata muhimmiyar tambaya ga Barret a kan ra’ayinta cewa, wanihukumcin da kotun koli ta yanke a shekarar 2012 na amincewa da dokar tsarin kiwon lafiya, dokar nan ta kasa da miliyoyin Amurkawa ke amfana da ita, da ta ce kuskure ne.

Kotun tana nazarin sake kalubalantar dokar kiwon kafiya a ranar 10 ga watan Nuwamba, lokacin da Barret ka iya zama daya a cikin alkalan kotun koli tara da zasu zartar da hukuncin ko dakatar da dokar ko kuma a ci gaba da aiki da ita.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG