Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Suna Kukan Rashin Kayan Aiki, Senata Ahmed Zanna Yace Ina Kudade Fiye Da Dala Milyan Dubu 10 da Aka Kasafta?


Wasu iyayen Chibok, Afrilu 29, 2014. (File Photo)
Wasu iyayen Chibok, Afrilu 29, 2014. (File Photo)

Senata Zanna ya bayyana fatar zuwan kasashen waje kan kokarin kubutarda 'yan mata 'yan makaranta zai kawo karshen rikicin.

Da yake magana da wakilin Sashen Hausa Saleh Shehu Ashaka senata Ahmed Zanna ya bayyana fatar zuwan kasashe kamar su Amurka da Britaniya da Fransa da sauransu, zai taimaka wajen kawo karshen rikicinda aka juma ana yi a yankin, ya janyo hasarar rayuka da raba dubban mutane da muhallansu da kuma hasarar dukiya mai dumbin yawa.

Da aka tambayeshi baya ganin cewa duk da shigowar wasu kasashen duniya domin taimakawa Najeriya, tilas sai da taimaka da hadin kan 'yan kasar kamin a shawo kan wannan rigima Senata Zanna yace muddin jami'an tsaron Najeriya suka hada kai da tawakrorinsu na kasashen waje ta ba za a fuskanci wata matsala.

Senata Zanna ya bayyana mamakin kan kukan rashin kayan aiki da sojojin najeriya suke yi duk da magudan kudade da aka kasafta dominsu cikin shekaru da suka wuce.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG