Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wani Gidan Azabtarwa A Jihar Adamawar Kasar Kamaru


An Gano Wani Gidan Azabtarwa A Jihar Adamawar Kasar Kamaru
An Gano Wani Gidan Azabtarwa A Jihar Adamawar Kasar Kamaru

Hukumomi sun bankaɗo wani gidan da ake azabtar da yara masu rashin ji na nufin tarbiyatar da su a anguwar hausawar Ngaoundere a Jihar Adamawa. Gwamnan jahar ya ce za'a dauki matakai masu tsanani kan jagororin waɗannan gidaje.

YAOUNDÉ, CAMEROON - ‘Yan sanda sun gano wani gidan azabtarwa a jihar Adamawar Kamaru, ƙarƙashin jagorancin gwamna Kildadi Taguiéké Boukar. Bincike ya bayyana mutum akalla 55 ke kulle a cikin wannan gida da ake yi wa kirarin cibiyoyin gyara halinka. Kamar bayi da sarƙa a hannu da ƙafa aka gano yara da matasa.

Mafi yawancin mutanen da aka gano a wannan gidan na da rauni da dama a jikin su.

Amma gwamna ya umurci ‘yan sanda da su kwance su sannan aka garzaya da su babban asibiti domin ba su kulawa. Gwamnan jihar Kildadi Taguiéké Boukar ya ce ba karon farko ba ne da hakan ke faruwa.

Ya ce za mu dauki tsauraran matakai wajen yanke hukunci kuma mun rufe wajen har sai bayan bincike. Baya da haka muna kiran iyayen yaran da su sake nazari kan tarbiyar 'ya'yansu. Da akwai hanyoyi da za a bi na karantar da yara.

Azabtarwa hanya ce da ake amfani da ita a da can, yanzu akwai hanyoyi na wayar da kan yaro zuwa don barin munana ɗabi'u. Da akwai kuma waɗanda suka ƙware wajen taimaka wa yara waɗanda ke neman lalacewa.

Wasu daga cikin matasan da aka garkame a gidan azabtawar sun shaida cewa an kai su ne domin zuwa makaranta amma sai suka tsinci kansu da sarka a kafa kuma ana azabtar da su sosai lamarin da ya kan kai wasunsu ga tabin hankali.

Daga cikin daliban, akwai wanda ya ce ya yi shekara daya da watanni biyu a wuri. Iyayen yaran da suka mutu ba su nemi su san ko mai ya faru ba.

Sarkin Hausawan Ngaoudere ya ce, shi bai jima da samun labarin wannan lamari na gidan azabtarwa ba.

Iyayen yara da yawa masu nema wa yaransu ko 'yan uwansu taimako saboda ta'amulli da miyagun ƙwayoyi ko wasu halayen marasa kyau sukan kai su cibiyoyin azabtarwan da nufin ayi musu magani.

Sai dai irin abubuwan da ake yi wa mutane a wadannan cibiyoyin sun haɗa da keta hakkin dan adam da cin mutunci.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mohamed Bachir Ladan:

An Gano Wani Gidan Azabtarwa A Jihar Adamawar Kasar Kamaru
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG