Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru: Hukumar Lafiya Ta yi Gargaɗi A Game Da Magungunan Jabu


Magungunan Jabu.
Magungunan Jabu.

Hukumar Lafiya a Kamaru ta yi gargadi a game da yadda magungunan jabu suka cika kasuwannin kasar musamman a manyan garuruwa. Magungunan na samun ci gaba da karɓuwa ga waɗanda ke cewa ba su da halin sayan nagari a shagunan da suka dace saboda tsadarsu.

Yaoundé, Cameroon - Hukumar lafiya ta bayyana cewa waɗannan magunguna na jabu an fi samun su ne a manyan garuruwa musamman Yaoundé da Douala, sai kuma birnin Bafoussam da ke yammacin ƙasar.

Ministan lafiya Manaouda Malachie, a wani taron manema labarai da ya jagoranta a babban birnin Ƙasar, ya ce amfani da magungunan jabu ya shafi duniya, sai dai illolinsa na da yawa musamman a Kamaru. A saboda haka gwamnati za ta ƙarfafa matakai domin kare al'umma. Amfani da waɗannan magungunan na da hatsarin gaske.

“Abin ban haushi a nan shi ne masu sayar da waɗannan magunguna, za ka gansu suna zaune ba abinda da ya dame su da matsalar da maganin jabu ke haddasawa a lafiyar masu amfani da su. Yanzu za mu ci gaba da nasiha. Amma bayan haka zamu ƙarfafa yaƙi da su domin tarwatsa wannan mummunar sana'a, a cewar ministan.”

Sai dai masu sayar da magungunan basu gamsu da sanarwar ministan ba.

“Aƙalla ‘yan Kamaru 80 cikin 100 na amfani da waɗannan magunguna. Mu muna sauwaƙa musu farashi saboda tsadar rayuwa. Yanzu gwamnati ta ce za ta yake mu. Bai kamata a tarwatsa mana hanyar neman halak ba tare da an samar mana wata mafita ba,” a cewar wani da ya nemi a sakaya sunansa.

Hakazalika masu amfani da magungunan na jabu sun koka kan tsadar magani a manyan wuraren sayar da nagari.

Ko a makonnin da suka gabata sai da hukumomi a Kamaru suka kona tan 60 na magungunan jabu da aka kama a kasar.

Wani lauya da ya bukaci mu sakaye sunansa ya ce hukunci da dokoki da gwamnati ta tanada a kan masu sayar da magungunan jabu, baya da tsananin da zai iya zamowa hannunka-mai-sanda ga duk masu shirin shiga wannan mummunar sana’a.

Kafin gwamnati ta ayyana wannan dokar ta, zaɓi ya rage ga masu anfani da waɗannan magunguna.

Saurari cikakken rahoton Mohamed Bachir Ladan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG