Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wani Sabon Salon Samarwa Mayakan Boko Haram Mai


Hotunan jarkokin mai da aka kwace

Jami’an Kungiyar tsaron sa kai ta farin kaya da ake kira “Civil Defense” sun ce sun gano wai sabon salon samarwa kungiyar Boko Haram da man fetur ta kan hanyar Maiduguri zuwa Mafa.

Kwamandan mayakan kungiyar ta sa-kai, Alhaji Abdullahi Ibrahim ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai.

Kwamandan ya bayyana cewa, mutanen suna zuba man ne cikin motoci wadansu lokatai su cika jarkuna su dinke a cikin buhuna kafin su dauka su tafi bayan gari.

Rundunar ta kama mutane da jarkunan mai arba’in da uku banda wadansu goma sha bakwai da aka samu a cikin mota. Bisa ga cewar Kwamandan, wadansu lokaci mutanen sukan kera wai tanki na musamman a motocinsu suna zuwa gidajen mai na NNPC su sayi mai domin su fitar waje.

Alhaji Abdullahi Ibrahim yace mutanen sukan dauki man zuwa garin Ngwam a hanyar Mafa inda suke saukewa sai ‘yan kungiyar Boko Haram su fito daga jeji su bada kudi su kwashe.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Bi'u ya aiko daga Maiduguri, Najeriya:

an kama masu saidawa Boko haram mai-3:19"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG