Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wasu Muggan Makamai a Dajin Adamawa


Jirgin yakin Najeriya mai daukar sojoji da manyan makamai.
Jirgin yakin Najeriya mai daukar sojoji da manyan makamai.

Jami'an tsaro a jihar Adamawan Najeriya sun gano wasu muggan makamai a wani dutse da ake kyautata zaton mabuyar 'yan bindigar da su ka gudo daga Zamfara ne.

Rundunar hadin gwiwa ta sojoji da 'yan sa kai a jihar Adamawa ta Najeriya sun yi nasarar tarwatsa mafakar masu tada kayar baya a karamar hukumar Maiha da ke jihar ta Adamawar.

Bayan da wasu 'yan gari su ka lura da wasu take take, da kuma wani bakon yanayi a wajejen wani dutse da ke dajin Maiha ne su ka sanar da jami'an tsaro da 'yan sa kai. Nan da nan ne sai jami'an tsaro da 'yan sa kai din su ka dunguma zuwa kan dutsen, inda suka kwato bindigogi masu kakkabo jiragen sama goma da kuma boma bomai a kan dutsen, wanda ke tsakanin Najeriya da Janhuriyar Kamaru.

Ana kyautata zaton miyagun sun gudo ne daga jihar Zamfara inda ake wuta ma 'yan bindiga ba ji ba gani.

Ga Muhammad Salisu Lado da cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00


XS
SM
MD
LG