Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari, Atiku Sun Yi Allah-wadai Da Kisan Mutum 24 A Adamawa


Gwamna jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, hagu da Atiku Abubakar, dama (Facebook/Gwamnatin Adamawa)
Gwamna jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, hagu da Atiku Abubakar, dama (Facebook/Gwamnatin Adamawa)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da harin da aka kai a yankin Hong da ke jihar Adamawa, harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 24.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannu kakakinsa Malam Garba Shehu, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wadanda suka aikata wannan aiki ba za su tafi salim-alim ba.

“Irin wannan rashin imani da rashin tausayi da ake nunawa akan bil adama, ba za a bar shi ya tafi ba tare da hukunci ba.” Buhari ya ce.

Ya kara da cewa, “ba zai yi wu mu yi kasa a gwiwa a idon ‘yan Najeriya ba wadanda suka damka mana amanar tsaronsu a hannunmu.”

A gefe guda, shi ma tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya yi tir da wannan hari.

Karin bayani akan: Atiku Abubakar, Adamawa, Boko Haram, Boss Mustapha, PDP, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“Ina mutukar Allah-wadai da kisan mutanen da aka yi a wasu sassan jihar Adamawa. Rayuwar dan adam tana da mutukar daraja.” Atiku Abubakar ya ce cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook.

“A matsayinmu na 'yan Najeriya, muna da nauyi dake kanmu ta hanyar aiki tare da gwamnatoci a dukkan matakai domin tabbatar da ganin an kawo karshen wadannan hare-hare.

“Ina mika sakon ta'aziyya ga wadanda suka rasa 'yan uwansu.”

Da sanyin safiyar Laraba wasu ‘yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne, suka kai hari kan wani yankin Dabna da ba shi da nisa da garin Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi tare da kona gidaje. Dabna gari ne da ya yi fice a harkar noma.

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG