Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda, Sun Yin Garkuwa Da Mutum 23 A Kaduna


'Yan Bindiga
'Yan Bindiga

Bayan kashe dan sandan, yan bindigar sun tafi da mutane 7 a unguwar Laka, ciki har da matar dan sandan da suka kashe da 'yarsa guda daya.

A jiya Laraba ne wasu 'yan bindiga da ba’a san ko su waye ba suka kai hari a unguwar Maje da Laka duk a karamar hukumar mulkin Chikun da ke jihar Kaduna inda suka kashe wani jami’in dan sanda har lahira tare da yin garguwa da wasu mutane 23.

A cewar wani shaidun gani da ido, 'yan fashin da suke dauke da muggan makamai, sun aukawa al'ummomin yankin inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa mutane suka yi ta gudu don tsira da rayukansu.

Da farko dai yan bindigar sun kai hari ne a unguwar Maje inda suka yi garkuwa da mutane 16, ciki da har da mata da yara kanana.

Bayan nan kuma sai su ka garzaya unguwar Laka inda suka kashe jami’in dan sanda mai suna Joshua Markus, wanda ya kawo wa iyalansa ziyara daga jihar Ribas.

Bayan kashe dan sandan, 'yan bindigar sun kuma tafi da mutane 7, ciki har da matar dan sandan da suka kashe da 'yarsa guda daya.

An sha fuskantar kalubalen tsaro kama daga hare-haren 'yan bindiga, har ya zuwa rikicin kabilanci da na addini a karamar hukumar ta Chikun da ke jihar Kaduna.

Jihar ta Kaduna kuma na daga cikin jihohin Arewa maso yamacin Najeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro, inda ake yawan samun rahotannin kashe-kashe da sace-sacen mutane a kusan kullum.

XS
SM
MD
LG