Wannan kira da kungiyar tayi ya biyo ne bayan wani sabon hari da aka kai a unguwar Mailafiya ta karamar hukumar mulkin Jama’a a kudancin jihar Kaduna. Kafin wannan hari a jajibirin bukin Kirsemeti, an dauki lokaci ba a kara jin wani hari ba a kudancin Kaduna da ya saba ganin tashe tashen hankula.
Sheikh Haliru Abdullahi Maraya na kungiyar Global Peace Foundation ya nuna takaicinsa ganin babu wanda aka taba gurfanar da shi gaban doka a sanadin tashe tashen hankula da aka saba gani a jihar Kaduna. Sheikh Abdullahi yace akwai bukatar farfado da tsarin iyayen kasa wanda kafin hukuma ta dauki mataki, su wadannan masu unguwa zasu iya tsawatawa.
Shima Reverend Joseph John na Peace Foundation yace akwai bukatar shiga cikin mutane domin a jawo hankalinsu a kan muhimmancin zaman lafiya.
Babban mai magana da yawun gwamnan Kaduna, Samuel Aruwan ya jajantawa yan uwa da abokan arziki na wadanda suka mutu a cikin rikicin. Yace gwamnati zata ci gaba da yin hadin gwiwa da jami’an tsaro wurin kare lafiyar al’ummar jihar.
Facebook Forum