Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gargadi Yahudawa Su Zauna da Shiri Saboda Harin Falasdinawa


Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gargadi Yahudawa da su zauna cikin shirin ko ta kwana da lura ainun game da wasu harin ta’addanci da rigingimu.

Ya fadi haka ne jiya Laraba bayan da wasu Falasdinawa suka kai hare-hare da wukake da duwatsu kan Yahudawa.

Yace fararen hula na kan gaba wajen yaki da ta’addanici, dole su lura ainun inda suke zaune domin kada ‘yan ta’ada su sha dasu.

A ziyararsa ga rundunar ‘yan sandan kasar ya jaddada wannan sannan kuma ya soke ziyararsa zuwa Jamus a yau Alhamis domin ya kalubali kowane irin yunkuri na sabon hare-hare Falasdinawa ka iya yin kokarin aunawa kan Yahudawan Isra’ila.

A jiya dai Laraba ne wata Bafalasdiniya ta soki wani dan Isra’ila da wuka wanda daga baya ya harbeta tare da ji mata ciwo a bangaren tsohon garin Jerusalem.

Harin ya biyo bayan sa’o’i bayan da Isra’ila ta sassauta dokar tsananin tsaro a kan Falasdinawan dake tsohon birnin.

XS
SM
MD
LG