A wata sanarwar da mataimakinta, Abdur-Rahman Balogun ya fitar a Abuja, Dabiri-Erewa ta ce abin damuwa ne ganin yadda ake samun karin kashe ‘yan Najeriya musamman mazauna birnin Landan.
"Yawaitar kashe bakaken fata, musamman 'yan Najeriya a Landan, ya zama babban abin damuwa" Sanarwa ta bayyana.
Rahotanni na nuni da cewa, a farkon shekarar 2018 kawai, an kashe ‘yan Najeriya sama da 50 wadanda aksarinsu matasa ne ta hanyar daba musu wuka ko kuma aka bindigesu.
Dabiri-Erewa ta shaida cewa ta isar da bukatar bi musu hakkinsu ga babban jakadan Birtaniya a Najeriya.
Wannan sanawar na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Buhari ke halartar taron kasashen da Ingila ta raina a birnin na London. A lokacin wannan ziyarar, ana sa ran zai gana da Firai Minista Theresa May.
Facebook Forum