Accessibility links

An Girke Sama Da Jami'an Tsaro Dubu A Minna

  • Grace Alheri Abdu

Jamia'an Tsaron Najeriya

Rundunar ‘yan sandan jihar Naija dake tarayyar Najeriya, tace ta sha damara domin ganin cewa, an gudanar da bukukuwan sallah lafiya a jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Naija dake tarayyar Najeriya, tace ta sha damara domin ganin cewa, an gudanar da bukukuwan sallah lafiya a jihar.

Rundunar ‘yan sandan tace yanzu haka an girke sama da ‘yan sanda dubu daya a Minna fadar gwamnatin jihar domin, dakile duk wani yunkurin tada hankalin jama’a a lokacin bukukuwan karamar Sallah da nufin ganin an gudanar da sallah lami-lafiya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Naija, Mr. Richard Adamu ya yiwa wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari karin haske dangane da shirin. Bisa ga cewarshi, rundunar tayi shirin hada hannu da ‘yan kasuwa domin ganin an yi sallah lafiya, banda haka kuma rundunar zata shiga kafar wando daya da ‘yan daba, ta kuma bayyana cewa, zata kama duk wanda ta gani ya fita da makami.

XS
SM
MD
LG