Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Gagarumar Zanga Zanga a Malawi


Masu zanga zanga a Malawi

Dubun dubatan ‘yan kasar Malawi ne suka fita zanga-zanga a jiya Alhamis, domin nuna kin amincewarsu da yunkurin da wasu suke yi na baiwa masu shari’a cin hanci a kan wata shari’ar da ake yi don kalubalantar sake zaben shugaba Peter Muthirika a bara.

Mutane sun dauki wannan matakin ne bayan da babban mai shari’ar kasar ya ce an baiwa Alkalai biyar da ke sauraron karar cin hanci.

A ranar Litinin ne aka kai karar gaban hukuma mai yaki da cin hanci a kasar, abin da ya yi sanadin soma wannan zanga-zangar a manyan biranen kasar uku.

Kimanin mutane 50,000 suka taru a babban birnin kasar Lilongwe, inda wasu tsiraru kuma suka taru a birnin Blantyre da Mzuzu.

Shugabannin adawa sun ce, anyi zamba a zaben da aka gudanar a ranar 21 ga watan Mayun bara, inda Mutharika ya yi nasarar doke abokin karawarsa Lazarus Chakwera da dan tazarar da bai taka kara ya karya ba.

A watan Agusta, shugabanin adawar suka kalubalanci babbar kotun Malawi a bisa sakamakon zaben, wannan shine karon farko a Malawi da za a kalubalanci zaben shugaban kasa a kotu tun da kasar ta samu ‘yancin kai daga Birtaniya a shekara ta dubu daya da dari tara da sittin da hudu.

Facebook Forum

Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG