Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Lahadi Muslim Brotherhood Zata Yi Shawarwari Da Gwamnati


Dattijan Muslim Brotherhood ake gani daga tsakiya suka shiga jerin masu zanga-zanga a Alkahira.
Dattijan Muslim Brotherhood ake gani daga tsakiya suka shiga jerin masu zanga-zanga a Alkahira.

Babbar jam’iyya dake hamayya a Masar, Muslim Brotherhood,tace zata fara shawarwari da mataimakin shugaban kasar, Omar Suleiman kan ‘yancin walwalarda jama’a suke da shi na yin zanga zanga.

Babbar jam’iyya dake hamayya a Masar, Muslim Brotherhood, tace zata fara shawarwari da mataimakin shugaban kasar, Omar Suleiman kan ‘yancin walwalarda jama’a suke da shi na yin zanga zanga,da kuma zancen shugaban Hosni Mubarak ya yimurabus.bayan shekaru 30 yana mulkin kasar.

Mataimakin shugaban kasa Suleiman,ya gana da wasu magoya bayan ‘yan hamayya,sai dai wan nan ne karo na farko da Muslim Brotherhood zata shiga shawarwarin.

Masu zanga-zangar nuna kyamar gwmnati sun cika dandalin Tahrir dake Alkahira fiyeda kwanaki 12,suna kira da shugaba Mubaraka ya yi murabus. Shugaba Mubarak yaki,amma ya fada cewa ba zai sake takara cikin watan satumba.

Jiya Asabar babban kwamitin gudanarwar jam’iyya mai mulki ya ajiye aiki.Tashar talaibijn ta kasar ta bada laabrin cewa wakilan kwamitin tsara manufofin jam’iyyar NDP mai mulkin Masar duk sun yi murabus,ciki har da 'dan shugaban kasar Gamal Mubarak. Duk da haka rahoton yace har yanzu shugaba Mubarak yana ci gaba da rike mukaminsa na shugaban jam’iyyar.

Rahoton yace babban sakataren jami’yyar Safwat el-shariff ya yi murabus kuma tuni aka maye gurbinsa.Rahotanni daga kafofin yada labaran kasashen yammacin Duniya sun bada labarin cewa kwamitin mai wakilai shida sune da jumawa jiga jigan siyasar Masar.

XS
SM
MD
LG