Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Halaka Masu Ibada 20 a Mujami'ar Masar


Wasu mabiya addinin Kirista masu ra'ayin gargajiya suna addu'ar ban kwana ga wasu matata
Wasu mabiya addinin Kirista masu ra'ayin gargajiya suna addu'ar ban kwana ga wasu matata

Wata fashewa da ta auku a wani cocin Kiristoci masu ra'ayin gargajiya a kasar Masar, ta halaka mutane 20 sannan wasu 35 sun jikkata.

Babu dai wanda ya dauki alhakin wannan hari da aka kai a yau Lahadi a Gundumar Abbassia da ke birnin Alqahira.

Amma kamfanin dillancin labaran kasar ta Masar, MENA, ya ruwaito cewa wani mahari ne ya jefa bam a cocin mai suna St. Mark’s.

Wakilin Muryar Amurka da ya ziyarci yankin da lamarin ya faru, ya ce harin ya auku ne da misalin karfe 10 na safen aogogn yankin, yayin da masu ibada wadanda mafi yawansu mata ne suke addu’oi.

Shugaba Abdel Fatah alsisi, ya ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku a kasar ta Masar, tare da mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su.

Cocin na St. Mark's matattara ce ga Kiristoci masu bin akidar gargajiya a kasar ta Masar, kuma gida ne ga shugabansu, Pope Tawadros II, wanda a lokacin harin ya ke ziyara a kasar Girka.

Masu rajin kare hakkin bil'adama da kafofin yada labarai sun jima suna fitar da rahotanni kan masu nuna kiyayya ga Kiristoci a kasar Masar.

A shekarar 2011 ma an kai wani hari a lokaicn bikin sabuwar shekara a wani Coci da ke Alexandria, wanda ya halaka mutane 20.

Kiristoci masu ra'ayin gargajiya, na da kashi 10 na yawan al'umar kasar ta Masar mai yawan mutane miliyan 93.

XS
SM
MD
LG